Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton duniya kan matsayin talaucin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton duniya kan matsayin talaucin Najeriya

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta yi watsi da rahoton da aka yi kan Najeriya a matsayin sauwar hedkwatar talauci a duniya inda aka ce ita ke da mafi yawan talakawa a duniya.

Bincike da kuniyar Brooking wacce ke birnin Washington DC, Amurka ta gudanar, wanda aka wallafa a maon da ya gabata ta bayyana Najerya a matsayin wacce ta haye kasarIndiya ta fannin talauci a 2018 inda a ko wani minti mutane 6 ke zama matalauta.

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton duniya kan matsayin talaucin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton duniya kan matsayin talaucin Najeriya

Sai dai da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan zaman mako na majalisar zartarwa,wana shugaban kasa Muhammadu Buhari ya agoranta a Abuja, ministan kasuwanci da zuba jari, Dr. Okechukwu Enelamah ya yi korafin cewa babu mamaki anyi amfani da lamuran lokacin da Najeriya ke cikin koma bayan tattalin arziki wajen hada rahoton.

KU KARANTA KUMA: Kisan Plateau: Masu zanga-zanga sun kai mamaya gidan gwamnati, sun lalata kayayyaki

Ya ce rahoton talaucin na iya kasancewa bisa ga la’akarin lokacina Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, tare da sawarar cewa kada kasar ta kashe kanta kan rahoton cewa talauci na karuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel