Rikicin jihar Filato: Muna sane sarai da abinda ake son kullawa - CAN

Rikicin jihar Filato: Muna sane sarai da abinda ake son kullawa - CAN

- Kungiyar Kiristoci (CAN) reshen jihar Bauchi ta yi magana a kan rikincin baya-bayan nan da ya barke a jihar Filato

- Kungiyar ta CAN ta bayyana cewar tana sane da cewar wasu mutane na kandagarki da makiyaya domin kashe jama'a

- CAN ta kara da cewar masu kashe-kashen na burin shafawa gwamnatin tarayya bakin fenti

Kungiyar kiristoci (CAN) reshen jihar Bauchi ta bayyana cewar dawowar kashe-kashe a jihar Filato munafurci ne da wasu makiya gwamnatin tarayya ke kullawa domin cimma manufar su ta siyasa.

Jaridar Tribune ta rawaito cewar shugaban kungiyar CAN reshen jihar ta Bauchi, Rabaran Joshua Ray Miner, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayyana ra'ayin sa a kan kashe-kashen jihar Filato a wata ganawa da suka yi da shi.

Rikicin jihar Filato: Muna sane sarai da abinda ake son kullawa - CAN
Zyarar shugabannin CAN ga shugaba Buhari

Rabaran Miner ya yi zargin cewar wasu 'yan siyasa dake burin ganin sun karbi mulki daga hannun gwamnatin tarayya ta kowanne hali, ke daukan nauyin kashe-kashen da ake yi a jihohin Filato da Benuwe da kuma arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Kar-ta-san-kar: Atiku da Obasanjo sun hadu a Abuja, kalli hotuna

"Akwai munafurci a cikin kashe-kashen, musamman idan ka kalli yadda ake kashe jama'ar da babu ruwan su, ta hanyar amfani da takobi, bindiga, da wuka domin a yaudaro jama'a, a nuna cewar Fulani ke aikata kisan.

"Wasu siyasa ne kawai ke fakewa da makiyaya domin shafawa gwamnatin tarayya bakinjini domin hatta masu aikata kashe-kashen an dauko hayar su ne daga kasashen dake makwabataka da Najeriya irin su Chadi, Mali, Nijar da Sudan," a cewar Rabaran Miner.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel