Kasashen musulmai guda 5 da zasu daina shiga kasar Amurka
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump ya nuna yanda ya samu gagarumar nasara a shirinsa da yake na hana bakin haure daga kasashe guda biyar na musulmi shiga kasar, sakamakon hukuncin da wata kotun koli ta amince da matakin da shugaban kasar ya dauka
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump ya nuna yanda ya samu gagarumar nasara a shirinsa da yake na hana bakin haure daga kasashe guda biyar na musulmi shiga kasar, sakamakon hukuncin da wata kotun koli ta amince da matakin da shugaban kasar ya dauka.
DUBA WANNAN: Zai yi shekaru 16 a gidan yari saboda ya bayyana ra'ayin sa a Facebook
Manyan alkalai guda biyar sune suka kada mashi kuri'ar goyon baya, a inda guda 4 suka nuna rashin amincewar su, hakan shine ya tabbatar da samun nasarar shugaba Donald Trump din a wannan takun saka da aka shafe tsawon watanni ana yi tsakanin shugaban kasar da wadanda suke kallon matakin a matsayin wanda ya sabawa dokar kasar Amurka, sannan kuma suke ganin kamar hakan zai shafi tattalin arziki da siyasar kasar dama duniya baki daya.
Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka zai shafi kasashen Yemen, Syria, Somalia, Libya da kuma kasar Iran, sai kuma kasar Koriya ta Arewa wacce shugaban kasar ya saka ta a cikin jerin kasashen.
Shugaba Trump yace ya dauki matakin ne domin tabbatar da tsaro ga kasar Amurka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng