Za'a fara Shari'ar Sufeto Janar na 'Yan sanda da Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Satumba

Za'a fara Shari'ar Sufeto Janar na 'Yan sanda da Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Satumba

Wata kotun tarayya dake garin Abuja a ranar Laraba da ta gabata ta kayyade watan Satumba lokaci na fara da sauraron takaddamar Sufeto Janar na 'yan Sanda, Ibrahim Idris, akan Majalisar dattawa da kuma shugaban ta, Abubakar Bukola Saraki.

Alkali Mai shari'a, John Tsoho, ya kayyade wannan rana ne bayan sauraron lauyan Sufeton na 'yan sanda, Alex Izinyon, wanda ya dage wajen rokon kotun kan ta amsa bukatar wanda yake yiwa wakilci.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Sufeton na 'yan sanda ya shigar da takaddamar ranar 9 ga watan Mayu har gaban Kuliya, inda Majalisar ta Dattawa ta aibata shi da cewar "Makiyi ne ga Dimokuradiyyar kuma bai cancanci rike shugabancin al'umma ba a ciki da wajen Najeriya".

Za'a fara Shari'ar Sufeto Janar na 'Yan sanda da Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Satumba
Za'a fara Shari'ar Sufeto Janar na 'Yan sanda da Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Satumba

A sanadiyar haka ne Sufeton na 'yan sanda yake rokon kotu kan ta tabbatar da adalci cikin wannan takaddama domin kuwa Majalisar dattawa ba ta da ikon bayyana tare da shellar rashin cancantar sa ta rike wani shugabanci na al'umma a ciki da wajen Najeriya.

DUBA WANNAN: Rashin adalci ne a ce na yi shiru kan Kashe-Kashen Makiyaya - Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, a baya Majalisar Dattawa da Shugaban na 'yan sandan Najeriya sun shiga takun saka da juna sakamakon rashin amsa goron gayyatar ta da Sufeton yayi a wasu lokuta daban-daban.

Sai dai Sufeton yayin wannan harkalla ya bayyana cewa ko kadan majalisar ba ta da hurumi ko iko cikin kundin tsari ko makamancin sa na gayyatar sa domin bayyana a gabanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng