Abinda Buhari da Lalong suka fadawa jama'ar Filato

Abinda Buhari da Lalong suka fadawa jama'ar Filato

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama dasu saboda ya san dukkan matsalolin da ke adabar kasar tun kafin ya tsaya takarar shugabancin kasar.

Shugaban kasar ya furta wannan magana ne a ranar Talata a gidan gwamnati yayin da ya ke jajintawa mutanen da aka kaiwa hari a Barikinladi, Riyom da wasu sassan kudancin Jos inda aka rasa rayyuka masu yawa.

"Na yi takarar shugababancin kasa har sau hudu kafin nayi nasara saboda haka ba zan iya yin korafi kan matsalolin da ake adabar Najeriya ba," inji shugaba Buhari.

Abinda Buhari da Lalong suka fadawa mutanen jihar Plateau
Abinda Buhari da Lalong suka fadawa mutanen jihar Plateau

Shugaban kasar ya cigaba da cewa gwamnatinsa da samu nasarori sosai a fanin samar da tsaro a kasar.

KU KARANTA: Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna

"Babu wanda zai iya cewa bamu tabuka komai ba a fanin samar da tsaro, munyi iya kokarinmu amma a halin yanzu abinda za mu iya yi shine addu'a," inji shugaban kasan.

Ya kuma yi kira da dukkan shugabani su zage damtse wajen gabatar da ayyukansu ga al'ummar yankunansu.

A bangarensa, gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya yi ikirarin cewa wasu bata gari ne da ke son tayar da fitina ne suka kai harin saboda suna son tayar da rikici a jihar," inji shi.

Gwamnan ya ce wasu mutane a jihar suna kokarin alakanta harin da addini musamman a Barikin ladi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen tsare lafiya da dukiyoyin al'umma a Jihar.

Gwamna Lalong ya yi ikirarin cewa wadanda suka kawo harin baki ne daga kasashen ketare.

"Bisa ga dukkan alamu irin makaman da akayi amfani dasu wajen kai harin ba suyi kama da irin makaman da ake amfani dasu wajen kare kai ba a kasar mu, hakan yasa muke tunanin wasu daga kasashen waje ne suka kawo harin," inji Lalong.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164