Asiri ya tonu: Sojoji sun kama 'yan leken asirin 'yan bindigan Zamfara

Asiri ya tonu: Sojoji sun kama 'yan leken asirin 'yan bindigan Zamfara

Sojojin Najeriya sunyi caraf 'yan leken asirin yan bindigan Zamfara uku a kauyan Gobirawa a ranar 25 ga watan Yuni sakamakon bayanan sirri da soji suka samu a kansu.

Ana zargin su da bawa yan bindigan bayanai kafin su kai hari a wasu kauyukan da ke Zamfara.

A halin yanzu ana cigaba da yi masa tambayoti kafin a mika shi hannun jami'an yan sanda kamar yadda kakakin hukumar sojin kasa, Brig. Janar Texas Chukwuma ya sanar.

Ta fara tonuwa: Sojoji sun kama dan leken asirin 'yan bindigan Zamfara
Ta fara tonuwa: Sojoji sun kama dan leken asirin 'yan bindigan Zamfara

KU KARANTA: Bayan sun gama soye wa ta sulale cikin dare da katinsa na banki, leka kuji nawa ta caje shi

Sojojin Operation Idon Raini kuma sun sun ceto wani da akayi garkuwa dashi a garin Abobo da ke karamar hukumar Dansadau tare da kwato babura guda hudu daga masu satar mutanen.

Masu satar mutanen sun tsere sun bar baburan nasu a yayin da suka hango motar sojojin daga nesa. Sojojin na cigaba da sintiri a kauyen don gano yan bindigan da suka tsere.

Hukumar sojin ta kara tunatar da mutane da su kai rahoton duk wani mutum ko ayyuka da ake gudanarwa da basu amince dashi ba.

A wata labarin Legit.ng ta ruwaito cewa wasu gungun yan bindiga dadi sun kashe dakarun rundunar Sojin kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da yan bindigar suka kai musu a cikin karamar hukumar Guma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun shirya wani tarko ne a daidai lokacin da Sojojin ke sintiri a a tsakanin kauyukan Umenger da Bakin korta, duk a cikin mazabar Mbadewem, a inda Sojoji biyu suka mutu, wasu kuma suka jikkata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164