'Yan sandan SARS sun lalata wa malamin makaranta kafa da harsashi

'Yan sandan SARS sun lalata wa malamin makaranta kafa da harsashi

Wani malamin makaranta a Jihar Ogun, Ola Hammed ya koka kan yadda jami'in dan sandan SARS ya lalata masa kafa bayan ya harbe shi a kafarsa ta hagu inda ya ke nema a bi masa hakkinsa.

Hammid ya ce dan sandan da ya harbe shi yana daya daga cikin yan sandan SARS da wasu 'yan unguwar Ibara da ke jihar Abeokuta suka jefa da duwatsu bayan sun yiwa wani mutum duka saboda yana daukan bidiyon yadda suke cin zalin wani mutum.

Ya yi ikirarin cewa jami'an Yan sandan sun bude wuta a kan mutanen, hakan kuma yasa masu wucewa da yan kasuwa suka tsere don kada harsashi ya same su.

'Yan sandan SARS sun lalata wa malamin makaranta kafa da harsashi a kafa
'Yan sandan SARS sun lalata wa malamin makaranta kafa da harsashi a kafa

Hammed ya ce dan sandan ya zargi cewa yana cikin wadanda suke jifan yan sandan duk da cewa ya fada masa baya cikinsu amma hakan bai hana dan sandan ya harbi shi a kafa ba.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Sojoji sun kama 'yan leken asirin 'yan bindigan Zamfara

Ya ce, "Rikicin ya afku ne a ranar 12 ga watan Yunin 2018. Rikici ya barke tsakanin wani mutum da jami'an FSARS a karkashin gadan Ibara a Abeokuta.

"Sun dauki sa'o'i suna rikicin kuma hayaniyar da su keyi ya janyo hankalin mutane masu wucewa, daga nan ne daya daga cikin yan sandan ya hango wani mutum na daukan bidiyo kuma ya matsa kusa dashi ya fara dukansa.

"Dukan da ya yi masa ne yasa mutanen da suka taru suna kallo suka fara jifan yan sandan da duwatsu. Daga nan kawai sai jami'an FSARS suka bude wuta suna harbin mutane da niyyar kashe su.

"Daya daga cikin yan sandan ya nufo ni inda ya ce ina cikin masu harbinsu duk da cewa bana ciki. Ina fada masa cewa ba ruwa na kawai sai ya ce zai lalata min kafa kuma ya harbe ni a kafa."

Daga nan ne aka garzaya da Hammed asibiti don yi masa magana. Hammed ya ce jami'an yan sandan suna zaluntar mutane kuma ya yi kira ga hukuma ta gudanar da bincike don bi masa hakkinsa.

Jaridar Punch ta yi kokarin tuntubar Hammed a shafinsa na Facebook da kuma wayarsa amma bai amsa ba har yanzu sai dai ya saka hoton raunin da ya yi sakamakon harbin da dan sandan ya yi masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164