Ta faru ta kare: Abubuwa guda 3 da suka cuci Najeriya a wasanta da Ajantina

Ta faru ta kare: Abubuwa guda 3 da suka cuci Najeriya a wasanta da Ajantina

A daren jiya ne kungiyar kwallon kafa ta kasar Ajantina ta yi ma kungiyar Super Egales ta Najeriya yankan kauna, wanda hakan ya kawo karshen cigaba da fafatawar Najeriya a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018 dake gudana a kasar Rasha.

Dayake wasa ne da ya dauki hankalin yan kallo tun kafin a buga shi, don haka ya sha nazari daga masana kwallon kafa a kafin fa kuma bayan wannan wasa, da wannan ne Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin abubuwan da suka bada gudunmuwar sallamar Najeriya daga gasar;

KU KARANTA: Manyan dillalan wiwi guda 88 sun fada komar jami’an hukumar NDLEA

1- Matsalar Ighalo:

Rashin takamaimen sahihin dan wasan gaba a kungiyar kwallon Super Eagles ta Najeriya ya zamo babban nakasu, sakamakon yan Ahmed Musa gefe yake bugawa, shi kuma Kelechi Iheanacho an cire shi tun a hutun rabin lokaci, wanda hakan ya bar kungiyar da Odion Ighalo, wanda ya samu damammaki har guda biyu masu kyau, daga shi sai gola, amma ya gagara zura kwallo ko daya, hakan ya sa bashi da kwallo ko daya a gasar gaba daya.

Ta faru ta kare: Abubuwa guda 3 da suka cuci Najeriya a wasanta da Ajantina
Ighalo

2- Alkalanci:

A gaskiya yan Najeriya basu yi dacen Alkalanci a wasansu da Ajantina ba, musamman duba da lokacin da mai tsaron gidan kasar Ajantina ya sanya ma wata kwallo hannu, kuru kuru kowa na gani, amma Alkalin wasan ya sanya ma idanunsa toka, duk kuwa da cewa fasahar bidiyo da ake amfani da shi ya tabbatar da laifin, amma ina, Alkali yace babu.

3- Wasan tsoro:

Kusan tun daga farkon wasan, yan wasan Najeriya sun nuna karaya da yan wasan Ajantina, watakila ganinsu Messi, Di Maria, Rojo da Higuain ne ya sanya musu tsoro a ransu, wanda hakan yasa suka koma suna wasan tsoro, irin na tsaron gida, gudun kada a cisu, amma duk da haka sai da aka zura musu kwallaye biyu.

A yanzu dai a iya cewa ta faru ta kare, wai an yi ma mai dami daya sata, Najeriya ta fita daga rukunin D na gasar tare da kasar Iceland, yayin da kasar Croatia da Ajantina da suka tsallake zuwa zagaye na gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel