Gasar cin Kofin Duniya: Hotunan atisayen yan kwallon Najeriya

Gasar cin Kofin Duniya: Hotunan atisayen yan kwallon Najeriya

Tawagar yan kwallon Najeriya dake wakiltar kasar a gasar cin kofin Duniya dake gudana a kasar Rasha sun gudanar da atisaye a shirye shiryen karawa da kasar Ajantina a wasan rukuni na karshe, kamar yadda jaridar muryar Amurka ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata, 27 ga watan Yuni ne za’a fafata tsakanin Ajantina da Najeriya a babban birnin St. Petersburg na kasar Rasha, wasan da zai baiwa Najeriya damar haurawa mataki na gaba, idan ta samu nasara akan Ajantina.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

Gasar cin Kofin Duniya: Hotunan atisayen yan kwallon Najeriya

Atisaye

A wasan Najeriya na farko ta samu rashin nasara a hannun Crotia, inda ta lallasa kasar Island ci biyu da babu, wanda hakan ya kai Najeriya matsayi na biyu a rukunin D da maki uku, biye da kasar Croatia mai maki shida, yayin da Ajantina ke da maki 1, Island ma maki 1.

Yan Najeriya na sa ran zasu samu nasara akan Ajantina sakamakon Ajantinan bata ci wasa ko daya ba, duk da cewa akwai manyan yan wasa a kungiyar kamar su Messi, Aguero, Higuain, Dimaria da dai sauransu.

Gasar cin Kofin Duniya: Hotunan atisayen yan kwallon Najeriya

Atisaye

Gasar cin Kofin Duniya: Hotunan atisayen yan kwallon Najeriya

Atisaye

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel