Ali Nuhu ya yi wa abokansa da sauran yan Super Eagles fatan alkhairi

Ali Nuhu ya yi wa abokansa da sauran yan Super Eagles fatan alkhairi

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen karawa tsakanin kungiyar kwallonkafa ta Najeriya wato Super Eagles da Argentina, shahararren dan wasan nan na Kannywood, Ali Nuhu wanda aka fi sani da sarki mai Sangaya ya yi wa yan Najeriya fatan alkhairi.

Jarumin ya wallafa a shafinsa domin karfafawa abokansa Musa da Shehu gwiwa da ma sauran yan wasan.

Ya rubuta: "Ina maku fatan alkhairi @shehu.official @ahmedmusa718, Allah ya ba ku da sauran tawagar nasara."

Ali Nuhu ya yi wa abokansa da sauran yan Super Eagles fatan alkhairi
Ali Nuhu ya yi wa abokansa da sauran yan Super Eagles fatan alkhairi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya Abdullahi Shehu ya bayyana cewa basa jin tsoron haduwa da fitaccen dan wasan Argentina Lionel Messi a karawar da za su yi a gasar cin kofin duniya.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

Kungiyar Super Eagles dai zata kara da Argentina a yau Talata, 26 ga watan Yuni.

Wasan ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar yayin kowace take neman yin nasara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng