Amurka tayi Allah wadai da kashe-kashen da a kayi a Filato
Amurka ta yi Allah wadai da kashe-kashen da akayi a Filato inda a kalla mutane 86 ne suka rasa rayyukansu kuma wasu da dama suka jikkata.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin Heather Nauret ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciko wadanda suka aikata kisan kana a gurfanar da su gaban kuliya.
KU KARANTA: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa
"Kasar Amurka tayi tir da kashe-kashen fararen hula da asarar dukiyoyi da akeyi a yankin tsakiya ta Najeriya a karshen makon da ya wuce.
"Muna damuwa kan yadda ake kara samun barkewar rikici kuma muna kira da dukkan shugabanin siyasa da na gargajiya su hada karfi da karfe wajen kawo karshen wadannan rikice-rikicen.
"Muna tarayya da shugaba Buhari da sauran mutane wajen mika ta'aziyyar mu ga al'umomin da wannan iftila'i ya shafa kuma muna fata za'a hukunta wanda suka aikata abin don kare afkuwar hakan a gaba," inji Nauret.
A cewar Terna Tyopev, kakakin hukumat Yan sanda na jihar Filato, an kone gidaje 50 da motocci biyu da kuma babura 15 a harin da makiyaya suka kai.
An ruwaito cewa makiyayan sun kai hari ne a unguwanin Razat, Ruku, Nyarr, Kura da Gana-Ropp da ke yankin Gashish a karamar hukumar Barikin Ladi a jihar ta Filato.
An saka dokar takaita fita waje a Riyom da Barikin Ladi da karamar hukumar Jos ta yamma bayan afkuwar hare-haren.
Shuagaba Buhari ya yi tir da harin kuma ya ce za'a binciko dukkan masu hannu don a hukunta su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng