Mutane 23 sunji munanan raunuka sanadiyyar hadarin mota a wani kauye dake kan hanyar Abuja
Wani hadarin mota daya afku a kan hanyar kauyen Kwaita dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, yayi sanadiyyar kwantar da mutane 23 cikin jini
Wani hadarin mota daya afku a kan hanyar kauyen Kwaita dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, yayi sanadiyyar kwantar da mutane 23 cikin jini.
Mutane 12 sun samu munanan raunuka, a lokacin da wata mota mai daukar mutane 18 ta fadi a ranar Asabar dinnan, yayinda wata mota mai kirar Toyota Previa mai rijistirashin lamba FST 927 XP ta fada cikin wani rami, inda mutane 11 suka samu raunuka daga cikin ta a ranar Juma'ar nan.
DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Za'a fara aikin wata babbar hanya data hade jihohi 3 a arewacin kasar nan
Wani wanda aka yi abin a gaban shi ya shaidawa manema labarai cewar, motar ta kwace daga hannun direban motar inda ta fada wani rami, sanadiyyar da mutane 11 suka ji munanan raunuka.
Ya ce daga baya jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa sun karaso wurin, inda suka wuce da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa.
Da aka tuntubeshi, shugaban hukumar yaki da haduran na Yangoji, ACC Samgbaza Joseph, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewar hadarin ya faru ne sanadiyyar gudun ganganci da direban yake yi.
A karshe ya ce, hukumar ta wuce da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibiti dake Kwali domin karbar magani.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng