Labari mai dadi: Za'a fara aikin wata babbar hanya data hade jihohi 3 a arewacin kasar nan

Labari mai dadi: Za'a fara aikin wata babbar hanya data hade jihohi 3 a arewacin kasar nan

Ministan wuta, ayyuka da gidaje na Najeriya Babatunde Fashola yace zai kaddamar da aikin gyaran babbar hanyar Kano zuwa Abuja a yau Talatar nan

Labari mai dadi: Za'a fara aikin wata babbar hanya data hade jihohi 3 a arewacin kasar nan
Labari mai dadi: Za'a fara aikin wata babbar hanya data hade jihohi 3 a arewacin kasar nan

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware kudade fiye da naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin gyaran hanya mai tsawon kilomita sama da 400, wacce ta tashi daga babban birnin tarayya zuwa Kaduna, sannan ta tsaya a Kano.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Sarki a wata jiha a kasar nan

A shekarara data gabata ne gwamanatin kasar nan ta amince da aikin hanyar, bayan wani zama da majalisar ministocin kasar nan suka yi a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hanyar dai ta jima da lalacewa dalilin da yake janyo hadarin motoci da dama a wasu wuraren, sannan akan samu asarar rayuka da dama sanadiyyar haduran da ake samu.

Jama'a da dama masu bin hanyar sunyi ta faman yin korafi akan yanda hanyar ta lalace kuma gwamnati ta nuna halin ko in kula akan gyaran hanyar.

A shekarar data gabata ne gwamnatin tarayya ta gyara hanyar wacce ta tashi daga Abuja zuwa Kaduna, dalilin rufe filin jirgin sama da aka yi na Abuja, domin gyaran filin jirgin. Sai dai kuma ba a jima ba hanyar ta sake lalacewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel