An bayyana wadanda za su kara da Najeriya idan sun yi nasara a Gasar World Cup

An bayyana wadanda za su kara da Najeriya idan sun yi nasara a Gasar World Cup

Gobe ne Najeriya za ta fafata da Kasar Argentina a Gasar cin kofin Duniya da ake bugawa a Kasar Rasha. Idan har Najeriya ba ta sha kashi ba dai akwai yiwuwar ta isa zuwa zagaye na gaba a Gasar.

Najeriya dai za ta kara ne da Kasar Faransa ko kuma Kasar Denmark idan ta kai zagaye na gaba. A gasan da aka buga a 2014 dai Kasar Faransa ce tayi waje da Najeriya da ci 2-0 a irin wannan zagaye da ake sa rai Najeriya ta kai.

An bayyana wadanda za su kara da Najeriya idan sun yi nasara a Gasar World Cup

Watakila Najeriya za ta hadu da Faransa ko Denmark Gasar World Cup

A 1998 kuwa Kasar ta Denmark ce tayi waje da Najeriya daga Gasar inda ta lallasa ta da ci 4-1. A sahu na C dai Kasar Faransa da Denmark ne za su fito inda cikin su wani zai hadu da Super Eagles idan ta iya samun sa’a kan Argentina.

KU KARANTA: Wata kasa ta karrama 'Dan wasan Kasar Misra Mohammed Salah

A sahun na Najeriya kuwa dai, Kasar Kuroshia ta fito bayan ta yi nasara a wasanni 2. Argentina da Iceland su na da maki 1 ne bayan sun yi kunnen doki yayin da Najeriya ta ke a matsayi na biyu da maki 3 bayan ta ci wasan ta na biyu.

Yanzu haka dai Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai tattara ya wuce Kasar Rasha domin karawa Najeriya karfin gwiwa a wasan da za ta buga. Saraki dai ya halarci wasan da Najeriya ta doke a Icelanda a Ranar Juma’a.

Kwanaki kun ji cewa Mai horas da ‘Yan kwallon Najeriya na Super Eagles Gernot Roht ya bayyana yadda ‘Yan wasan sa za su yi su ba Kasar Argentina kashi a wasan karshe na zagayen farko na Gasar cin kofin na Duniya da ake bugawa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel