‘Yan bindiga sun kashe wasu Matasa a Jihar Katsina a cikin tsakar-dare

‘Yan bindiga sun kashe wasu Matasa a Jihar Katsina a cikin tsakar-dare

Dazu nan mu ka ji labari daga manema labarai cewa wasu ‘Yan bindiga dadi sun kashe wasu ‘Daliban Makaranta sun kuma dauke wani Bawan Allah sun yi gaba da shi a Jihar Katsina da ke Arewacin Kasar nan a Ranar Lahadin nan.

Ibrahim Bature da kuma Rabi’u Abubakar da ke karatu a Jami’ar Al-Qalam sun bakunci lahira ne bayan da wasu ‘Yan bindiga su ka shiga Kauyen Bagiwa da ke cikin Karamar Hukumar Mani a Jihar da Shugaban Kasa Buhari ya fito.

‘Yan bindiga sun kashe wasu Matasa a Jihar Katsina a cikin tsakar-dare

An hallaka wasu 'Yan makaranta a Jihar Katsina

Bayan haka kuma ‘Yan bindigan sun harbi Mahaifiyar daya daga cikin wannan Matasa da aka kashe mai shekaru 60 a Duniya. Alhaji Lawal Bagiwa ya bayyanawa manema labarai wannan a madadin iyalin wadanda su ka yi wannan rashi.

KU KARANTA: An yi ram da wani shugaban wata makaranta mai takardun boge

Alhaji Bagiwa ya kuma bayyanawa ‘Yan jarida cewa wadannan ‘Yan bindiga sun kuma yi gaba da wani Bawan Allah mai suna Umar wanda ‘dan uwan Matasan da aka kashe ne. An dai kai wannan hari ne cikin tsakar dare yayin da ake barci.

Jami’an ‘Yan Sanda ta bakin SP Isah Gambo ya tabbatar da cewa wannan mummunan abu ya faru inda kuma su kayi alkawarin kama wadanda su ka yi wannan ta’asa. Iyalan da su kayi wannan rashi dai sun ce har yanzu ba aji duriyar wanda aka sace ba.

Dazu ne kuma ku ka ji cewa hare-haren da aka kai a Garin Barkin Ladi da ke Jihar Filato a karshen makon nan yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 86 a tashi guda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel