Kauracewa babban taron APC da Kwankwaso yayi alamu na cewa harkar siyasarsa ya zo karshe – Garba
Kwamishinan bayanai na jihar Kano, Kwamrad Mohammed Garba, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan kauracewa babban taron APC da aka gudanar a Abuja a karshen mako.
A ranar Litinin, 25 ga watan Yuni, Garba ya bayyana hujjar da Kwankwaso ya bayar na kin halartan taron a matsayin karya.
A wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar ya ce dalilinsa na kauracewa taron ya kasance saboda baya son wani hargitsi ya taso.
Garba ya maida hankali kan cewa kamata yayin Kwankwaso yayi amfani da wannan taro a matsayin wata dama na gyara barakarsa da Gwamna Ganduje don jagorancin APC a Kano.
KU KARANTA KUMA: Rundunar soji sun tura jiragen yaki 7 zuwa Benue da Taraba
Ya kuma bayyana cewa rashin halartan Kwankwaso wajen babban taron ya nade harkar siyasarsa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng