In kana duniya kasha kallo: An gano wani kashin kunkuru mai shekaru miliyan 150 a duniya
An bayyana cewar an bankado wasu kasusuwan kunkuru mai kimanin shekaru miliyan 150 a yankin Chongching dake yankin kudu maso yammacin kasar China.
An tabbatar da cewar an bankado wasu kasusuwan kunkuru mai kimanin shekaru miliyan 150 a yankin Chongching dake yankin kudu maso yammacin kasar China.
Wani manomi dake zaune a yankin mai suna Lu'ulu'u Changyu shine ya gano kasusuwan kunkurun.
DUBA WANNAN: Yaron gida ya yiwa babban soja Bahaushe da budurwar sa kisan gilla
Diyar mutumin ta dauki hotunan kashin kunkurun inda ta yada a shafin ta na sada zumunta na WeChat.
Hukumar nazarin tsofaffin kayayyakin tarihi sun ga wannan kashi na kunkuru, inda suka fara bincike akan shi, daga baya suka bayyana cewar kashin kunkurun yana da kimanin shekaru miliyan 150 a duniya.
Daga karshe dai hukumar ta adana kashin kunkurun a gidan tarihin kasar ta China.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng