Hanyar da za mu bi mu lallasa Messi da Argentina – Kocin Super Eagles

Hanyar da za mu bi mu lallasa Messi da Argentina – Kocin Super Eagles

Mun samu labari cewa babban Mai horas da ‘Yan kwallon Najeriya na Super Eagles Gernot Rohr ya bayyana yadda ‘Yan wasan sa za su yi su ba Kasar Argentina kashi a wasan karshe na zagayen farko na Gasar cin kofin Duniya da ake bugawa.

Hanyar da za mu bi mu lallasa Messi da Argentina – Kocin Super Eagles
Rohr yace sirrin isa zagaye na gaba a World Cup shi ne a kai wa Argentina hari

Gernor Rohr wanda shi ke kula da ‘Yan wasan Najeriya yace idan Super Eagles ta hadu da Argentina a Ranar Talata za ta shiga kai wa Kasar hari ne babu dare ba rana idan fa har su na so su ga sun isa zagaye na gaba a Gasan na Duniya.

Rohr yace ba za su nemi ayi kunnen doki da Argentina ba domin hakan na iya zama matsala idan aka ci Najeriya daf da lokacin tashi kamar dai yadda Jamus tayi wa Suwidin a wasan jiya inda aka tashi 2-1 bayan Suwidin ta fara jefa kwallo.

KU KARANTA: Ruwa ya ci wasu yara a kududdufi daga kokarin zuwa wanka

Mai horas da ‘Yan wasan na Najeriya ya dai nuna cewa wasan Najeriya da Argentina zai yi zafi kwarai da gaske ganin cewa duk wanda yayi nasara yana iya kai wa zagaye na biyu muddin dai Kasar Iceland ba tayi wa Kuroshia cin kaca ba.

Idan dai aka tashi kunnen doki tsakin Najeriya da kasar ta su Lionel Messi, Super Eagles za ta iya karasawa zagaye na biyu. Shi dai Kocin na Najeriya yace nasara ya ke nema kamar yadda aka doke Iceland kwanan nan ba ma wai ya rike Argentina ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng