Rana ta biyu: Buhari, Tinubu da gwamnoni sun rabawa daliget mabanbantan sunayen ‘yan takarar da zasu zaba

Rana ta biyu: Buhari, Tinubu da gwamnoni sun rabawa daliget mabanbantan sunayen ‘yan takarar da zasu zaba

A yayin da zaben shugabannin jam’iyyar APC ya shiga rana ta biyu, daliget da zasu zabi sabbin shugabanni sun shiga rudani a kan sunayen ‘yan takara da aka basu daga masu a fada a ji a APC.

Wata majiyar jaridar Premium Times ta rawaito cewar an bawa daliget sunayen ‘yan takara 11 ta hannun shugaban kwamitin zaben, gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar. Ana zaton ceware jerin sunayen ‘yan takarar ya samu sahalewar shugaba Buhari.

Majiyar ta bayyana cewar shugaba Buhari ya shaidawa gwamna Badaru cewar ya tuntubi abokan sa, gwamnoni, domin su bayar da ragowar ‘yan takarar su da zasu cike ragowar guraben. A cikin jerin sunayen akwai Adams Oshiomhole a matsayin shugaba da Farouk Adamu Aliyu a matsayin sakataren jam’iyya na yankin arewa da kuma Mala Buni a matsayin sakataren jam’iyya.

Rana ta biyu: Buhari, Tinubu da gwamnoni sun rabawa daliget mabanbantan sunayen ‘yan takarar da zasu zaba
Buhari, Tinubu da gwamnoni sun rabawa daliget mabanbantan sunayen ‘yan takarar da zasu zaba

Saidai a gefe daya kuma an bawa daliget din wani jerin sunayen ‘yan takara daga bangaren jagoran jam’iyyar, Bola Tinubu. A cikin sunayen akwai Oshiomhole a matsayin shugaba da Lawal shu’aibu a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa da kuma Kashim Imam a matsayin sakataren jam’iyya. Saidai daga baya Imam ya janye daga takarar.

DUBA WANNAN: Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya

Kazalika an raba wani jerin sunayen day a fito daga hannun gwamnoni ga daliget din. Akwai sunayen mutane 35 a takardar dake dauke da sunayen. Akwai sunan Oshiomhole, Farouk Adamu da Niyi Adebayo a cikin sunayen.

Wasu daga cikin ‘yan takara da aka ga suanayen su sun hada da Bulama Waziri a matsayin sakatare, Fatima Adams a matsayin shugabar mata da Bolaji Abdullahi a matsayin sakataren watsa labarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng