Ruwa ya sake ajalin wasu yara guda 2 yayin wanka a kudiddifi
- Zuwa wanka rafi ko kududdifi na cigaba da zama sanadiyyar mutuwar yara a Jigawa
- Bayan waɗanda suka mutu a kwanan baya, wasu su sake sheƙawa barzahu
Wasu yara guda biyu sun gamu da ajalinsu a yayin da suke yin wanka a wani rafi dake ƙauyen Gansa a ƙaramar hukumar Buji a Jihar Jigawa.
Wasu yara guda biyu sun gamu da ajalinsu a yayin da suke yin wanka a wani rafi dake ƙauyen Gansa a ƙaramar hukumar Buji a Jihar Jigawa. Wasu yara guda biyu sun gamu da ajalinsu a yayin da suke yin wanka a wani rafi dake ƙauyen Gansa a ƙaramar hukumar Buji a Jihar Jigawa.
Mai magana da yawun hukumar tsaro ta fararen kaya Adamu Shehu ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Dutse, inda ya shaida cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 yamma.
Jami'in ya bayyana sunayen yaran da suka rasu da; Yusuf Adamu mai shekaru 6, sai Umar Ibrahim ɗan shekara 4, yace likita ne ya tabbatar da rasuwar su bayan an dauke su zuwa asibiti domin ceto rayukan su.
KU KARANTA: ‘Dan adaidaita-sahu ya tsula tsiya amma ya shiga hannu
Shehu ya yi kira ga iyayen yara a jihar da suke sanya ido sosai kan yaransu da kuma sanin wani irin nau'in wasa suke aikatawa domin gujewa wani iftila'i makamancin wannan.
Idan za a iya tunawa ranar 7 ga watan Disamba 2017 wasu yara yan mata har su hudu suma ruwa ya cinye su a yayin wanka a kauyen Sakwaya dake karamar hukumar Dutse.
Har wa yau, 8 ga watan Yulin 2017 mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Abdu Jinjiri ya shaidawa manema labarai cewa a duk wata akan samu yara daban waɗanda zasu kai mutum 11 da ruwa yake cinyewa a fadin jihar baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng