Ba za mu rangwantawa Kasar Argentina ba - Ahmad Musa

Ba za mu rangwantawa Kasar Argentina ba - Ahmad Musa

Ahmad Musa, Fitaccen dan wasa da ya jefa kwallaye biyu da suka tabbatar da nasarar kasar Najeriya yayin wasan kwallon kafa da ta kara da kasar Iceland a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, ko kadan ba za su ragawa kasar Argentina ba a wasan su na gaba.

A yayin wasan na gasar kofin duniya da aka kara a birnin Volgograd na kasar Rasha inda Najeriya ta lallasa kasar Iceland ci biyu da nema, ya karawa dan wasan Najeriya Ahmad Musa karfin gwiwa da yake ganin za su yi fatata da kasar Argentina idan su kara a wasan su na gaba.

Sai dai ko shakka babu Musa ya bayyana cewa, kasar Argentina ba kanwan lasa ba ce saboda haka sai sun nuna wa 'yan wasan ta rashin sani da sabo yayin haduwar su a wasa na gaba.

Musa wanda shine ya jefa kwallaye biyun da suka tabbatar da nasarar kasar sa ta Najeriya ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan an tashi wasan a birnin Volgograd kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana.

Ba za mu rangwantawa Kasar Argentina ba - Ahmad Musa

Ba za mu rangwantawa Kasar Argentina ba - Ahmad Musa

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, dan wasa Musa shine ya lashe kyautar zakakurin da ya fi kowa hazaka a wasan su da kasar Iceland a sakamakon jefa kwallayen sa a minti na 49 da kuma na 75 da ya tabbatar da nasarar Najeriya.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya sake sabbin nade-nade a Gwamnatin sa

Ko shakka babu Musa ya yi matukar farin ciki dangane da bajintar sa da kuma nasarar da kasar sa ta Najeriya ta samu a wasan na su da kasar Iceland. Sai da yace babban abinda ya mayar da hankali a halin yanzu shine wasan su da kasar Argentina da yace wuta-wuta za a buga shi.

Hakazalika Musa ya yi godiya ga 'yan Najeriya sakamakon goyon bayan da suka nuna kan kungiyar kwallon kafa ta kasar nan da hakan ya taimaka wajen matsa lamba ga 'yan wasan kasar Iceland.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan nasara ta tura Kasar Najeriya zuwa mataki na biyu da maki uku a gurbin su, inda kasar Croatia ke kan gaba da maki shida yayin da kasar Argentina da Iceland ke da maki daya ga kowanen su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel