Hukumar yan sanda ta damke fasto, wasu biyu da laifin amfani da karuwa wajen asiri
Hukumar yan sanda a jihar Kogi ta damke wani fasto mai suna, Oluwasegun Aturu, da wasu mutane biyu kan laifin kisan wata karuwa mai suna, Miss Mercy Moses, da kuma amfani da ita domin asiri.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP William Aya, ya tabbatar da wannan kamu ga manema labarai a garin Lokoja yau Juma’a.
Yace fasto Oluwasegun Aturu ya kasance shugaban cocin Voice of Canaan Temple, Cherubim and Seraphim Aladura Church, Ozuri a karamar hukumar Adavi a jihar Kogi ya shiga hannu ranan 19 ga watan Yuni.
An damke shi tare da Samuel Oluwasegun da Abdulmumini Yakubu a unguwar Ozuri a karamar hukumar.
KU KARANTA:
Game da cewar yan sanda, Oluwasegun da Yakubu sun tafi gidan magajiya ranan 11 ga watan Yuni misalin karfe 10 na dare domin daukan karuwa inda suka tafi da ita.
Yace: “Maza biyu sun sami wata Mercy Moses, daya daga cikin karuwan gidan. Bayan tattaunawa da ita, sai suka tafi da ita kan babur.”
“Bayan kwana biyu da manajan gidan magajiyan bai ganta ba, sai ya kai kara ofishin hukumar yan sanda da ke Adavi.”
Bayan bincike, an damke fasto Otaru, Oluwasegun da Yakubu amma suka musanta cewa basu santa ba.
“Amma bayan tambayoyi da muka yi, Oluwasegun da Yakubu sun bayyana yadda faston ya basu aikin kawo masa mace inda ya musu alkawarin N700,000”
Duk da cewa faston ya tsere, hukumar yan sanda sun samu nasarar damkeshi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng