Shahararren mai garkuwa da Mutane, Evans, ya yi hayar sabon Lauya

Shahararren mai garkuwa da Mutane, Evans, ya yi hayar sabon Lauya

Kasurgumin attajirin nan da ake zargi kan shahara da garkuwa da Mutane, Chukwudumeme Onwuamadike mai inkiyar nan ta Evans, ya sake hayar wani sabon lauya sakamakon janye wa daga shari'ar da tsohon Lauyan sa na asali ya yi, Olukoya Ogungbeje.

Sabon Lauyan, Noel Brown, ya bayar da sanarwar yiwa Evans wakilci tare da abokin aikin sa, Ogechi Uchechukwu a gaban Alkali Hakeem Oshodi yayin ci gaba da shari'ar a babban kotun jihar Legas dake Birnin Ikeja a ranar Juma'ar da ta gabata.

Shahararren mai garkuwa da Mutane, Evans, ya yi hayar sabon Lauya
Shahararren mai garkuwa da Mutane, Evans, ya yi hayar sabon Lauya

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Lauya Brown ya nemi Alkali Oshodi ya tabbatar da wakilicin sa daga bakin Evans a matsayin sabon lauyan sa inda ya kuma amsa da na'am.

KARANTA KUMA: Lalata da Kantar Rashawa ta kai kololuwa a Majalisar Dokoki ta Tarayya - Okurounmu

Sai dai a halin yanzu wadansu mutane biyu cikin wanda ake zargi da sanya hannun cikin wannan ta'addanci na garkuwa da Mutane tare da Ubangidan su Evans, sun gaza gabatar da wakilan su sakamakon janyewa da tsaffin lauyoyin su suka yi inda suke sa ran hayar wasu kafin zaman kotun na gaba.

A makon da ya gabata ne shafin Jaridar Legit.ng ya ruwaito cewa, lauya mai kare Evans a gaban kotu Olukoya Ogungbeje, ya janye daga shari'ar sakamakon barazanar da wasu al'ummar kasar nan ke yi ga rayuwar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel