Wani mai aski a Abuja ya dauki nauyin yiwa shugaba Buhari aski domin ragewa gwamnatin tarayya kasafin kudin kasar N86m

Wani mai aski a Abuja ya dauki nauyin yiwa shugaba Buhari aski domin ragewa gwamnatin tarayya kasafin kudin kasar N86m

Wannan karni da muke na shafukan zumunta ya bayar da damar da mutane da dama zasu iya tallata hajar su ga kowa duk kuwa da matsayinsu, hakan ce ta kasance ga yan Najeriya.

Wani mai yin aski dake zaune a Abuja wanda aka ambata da suna Alfred Umoh, ya je shafin zumunta domin gabatar da wata bukata a shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bisa ga rubutun da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace maimakon yin kasafin N86m na aski, shi ya dauki nauyin yiwa shugaban kasar aski a kyauta na tsawon shekara daya.

Wani mai yin aski a Abuja ya dauki nauyin yiwa Buhari aski domin ragewa kasafin kudin kasar N86m
Wani mai yin aski a Abuja ya dauki nauyin yiwa Buhari aski domin ragewa kasafin kudin kasar N86m

A cewarsa ayi amfani da kudin wajen gina dakunan shan magani na gwamnati guda 2 a jiharsa ta Akwa Ibom sannan a gina daya a Abuja kan naira miliyan 28 ko wane.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

Ya jadadda cewa ta wannan hanyan ne kadai zai iyta taimakawa gwamnati, cewa wannan gwamnatin na bukatar taimako sosai.

Ga yadda ya wallafa a shafinsa:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng