Lalata da Kantar Rashawa ta kai kololuwa a Majalisar Dokoki ta Tarayya - Okurounmu
Kamar yadda shafin jaridar Nigerian Tribune ya ruwaito, wani tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Femi Okurounmu, ya bayyana Majalisar Dokoki ta tarayyar kasar nan a matsayin farfajiya mafi muni ta fuskar gurbatanci na rashawa.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Okurounmu wanda ya wakilci mazabar jihar Ogun ta Tsakiya a tsakanin shekarar 1993 zuwa 2013 ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Abeokuta.
Tsohon shugaban kwamitin bayar da shawarwari ga shugaban kasa kan muhimman taro na kasa ya bayyana cewa, ko shakka ba bu 'yan Majalisar tarayya mayaudara ne masu hali na mazambata da ba bu abinda suka nufata face soyuwar zukatan su.
Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon dan majalisar ya kausasa harshe kan 'yan Majalisar sakamakon cushe na wani adadin kudi da suka aiwatar cikin kasafin kudin kasar nan domin samun dama ta karin wasu alawus da sabawa ka'ida domin biyan bukatun su na karan kansu.
Hakazalika Sanata Okurounmu bai tsarkake shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da wannan badakala dake tsakanin sa da 'yan Majalisar na tarayya ba, inda yace ya kasance tamkar sauna da ya zuba ma su idanu su na cin karen su ba bu babbaka.
A kalaman sa, "bugu da kari ba ya daga cikin halayyar kirki ace wadanda suka gurbata da rashawa su rika gindayawa kowace kasa doka. Ba bu mutanen da rashawa ta yiwa katutu a Najeriya tamkar 'yan Majalisar tarayya."
A yayin da manema labarai suka tuntube sa dangane da dalilin da ya sanya shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin duk da cushe da sauye-sauye da Majalisar tarayya da gudanar a ciki ya bayyana cewa, da fadar shugaban kasar da Majalisar sun kasance kashi biyu na 'yan Fashi.
KARANTA KUMA: An ci zarafin Yara 500 a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu - Jakadiyar UN
Yake cewa "Shugaba Buhari ba ya da wani zabi sakamakon Majalisar da ta kasa ta ba shi fata; ba zai iya watsar da su lokaci guda ba hakazalika ba ya da ƙarfin hali na yakar su gaba daya."
"Matukar yana da ƙarfin hali na yakar su zai iya, sai dai ba ya da shi sakamakon gurbatancin rashawa cikin mutanen da ke kewaye da shi."
Ya kara da cewa, "Kamar yadda Majalisar Tarayya ta yaudare shi, zai iya yaudarar ta tare da yi ma ta bi ta da kulli. Sai dai kamar yadda na shaida sun kasance 'yan Fashi ne kashi biyu."
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta gargadi gwamnatin tarayya kan taka tsantsan yayin kafa yankunan kiwon shanu a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng