Likafa ta cigaba: Wata Jami’ar kasar waje ta karrama Aisha Buhari da digirin digirgir

Likafa ta cigaba: Wata Jami’ar kasar waje ta karrama Aisha Buhari da digirin digirgir

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta samu lambar yabo daga wata jami’a dake kasar Koriya ta kudu, wanda suka ce ya zama wajibi su karramata sakamakon ayyukan alheri da na jin kai da take gudanarwa.

Legit.ng ta ruwaito sunan jami’ar da ta karrama Aisha Buhari, Sun Moon, kuma shugaban sashin ilimin kimiyyar siyasarta, Farfesa Hong Young-Shik ne ya jagoranci tawagar wasu shuwagabannin jami’ar zuwa fadar gwamnati dake Abuja a ranar Alhamis 21 ga watan Yuni, inda suka karramata da lambar yabo na digirin digirgir.

KU KARANTA: Kuma dai: an kwashi gawarwakin mutane 4 bayan da yan bindiga suka kai hari jihar Filato

Likafa ta cigaba: Wata Jami’ar kasar waje ta karrama Aisha Buhari da digirin digirgir
Digirin digirgir

“Irin ayyukan jin kai da Aisha Buhari ke yi ya janyo hakulan kasashen Duniya gaba daya, wannan yasa kwamitin koli na jami’ar Sun Moon ta ga dacewar karramata, musamman duba da yadda ayyukan nata ke shafar kananan Yara da Mata.

“Haka zalika mun yaba da salon kamun ludayin Maigidan Aisha Buhari, shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wajen tafiyar da al’amuran mulki, da wannan ne jami’armu ta umarceni da na baki lambar yabo ta girmama na digirin digirgir a sha’anin ayyukan jin kai ga al’umma.” Inji shi.

Likafa ta cigaba: Wata Jami’ar kasar waje ta karrama Aisha Buhari da digirin digirgir
Digirin digirgir

Da take nata jawabin, Aisha Buhari, wanda ta samu wakilcin hadimarta, Dar Haji Sani ta bayyana godiyarta ga jami’ar da ta fahimci irin kokarin da Aisha Buhari ke yi wajen inganta rayuwar Bil’adama, don haka ta amshi wannan lambar yabo, kuma ta sadaukar da shi ga mata da kananan yaran Najeriya.

Daga karshe Aisha Buhari ta dauki alwashin cigaba da inganta rayuwar Mata da kananan yara ta gidauniyarta mai suna ‘Future Assured’, wanda ke tallafa ma gajiyayyu cikin mata da kananan yara ta fannin ilimi, kiwon lafiya, basu kariya da kuma habbaka su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel