Da dumin sa: Buhari ya zubar da hawaye yayin da ya ziyarci kasuwar Azare da gobara ta lalata,kalli hotuna
Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi domin jajantawa mutan Azare a kan iftila'in gobara da ya faru a kasuwar garin.
Jirgin da ke dauke da shugaba Buhari ya dira a babban filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa ne misalin karfe 9:30 a yau Alhamis, 21 ga watan Yuni, 2018.
Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da kakakin majalisar dokokin jihar, Kawuwa Damina, suka tarbi shugaba Buhari a filin jirgin saman.
DUBA WANNA: An fara: Atiku ya fara rangadin neman goyon baya don tsayawa takara, ya nada sarkin yakin neman zaben sa
Sauran da suka tarbeshi sune Diraktan hukumar agaji na gaggawa wato NEMA, Mr Mustapha Maihaja; sakataren gwamnatin tarayya, Mr Mohammed Nadada, da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin jihar.
Shugaba Buhari ya kai ziyarar gani da ido kasuwar inda rahotanni suka bayyana cewar saida ya zubar da hawaye saboda tausayawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng