Tausayi: Buhari ya zubar da hawaye yayin ganin tsabar barnar da gobara ta yi a kasuwar Azare
A yau Alhamis, 21 ga watan Yuni ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi takakkiya daga fadar gwamnati dake Abuja zuwa garin Azare na jihar Bauchi domin jajanta ma al’ummar garin biyo bayan wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwa.
Wannan ibtila’I ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar kona shaguna sama da dubu daya kurmus, ba tare da masu su sun cire ko tsinke ba, haka zalika duk a wannan rana aka yi wani iska mai karfi da ruwan sama a garin Bauchi da ta lalata daruruwan gidaje, tare da jikkata mutane.
KU KARANTA: Kafa da kafa: Buhari zai kai ziyarar jaje Bauchi bisa ibtila’in da ta fada ma al’ummar jihar
Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido, kuma ma’abocin kafar sadarwar zamani, Usman Abdulmumin Liman ya tabbatar da cewa a lokacin da Buhari ya ga yadda wutar ta yi barna a kasuwar, sai da ya zubar da hawaye.
Sai dai ba wannan bane karo na farko da shugaba Buhari kezubar da hawaye a bainar jama’a, inda a yayin zaben shekarar 2011 ma ya zubar da hawaye sakamakon damuwa da yake ciki sakamakon halin da yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci.
Haka zalika a yayin zaben shekarar 2015, shugaba Buhari ya fashe da kuka sakamakon shaukin da ya dabaibaye shi a lokacin da ya hadu da wata tsohuwa mai kaunarsa a jihar Kebbi, marigayiya Hajia Fadimatu Mai Talle Tara, wanda ta bashi gudunmuwar naira miliyan daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng