‘Dan adaidaita-sahu ya tsula tsiya amma ya shiga hannu

‘Dan adaidaita-sahu ya tsula tsiya amma ya shiga hannu

- Wasu gugun matasa da suka hada baki wajen haikewa wata 'yar mitsilar yarinya sun shiga uku

- 'Yan sanda sun baza komarsu domin nemansu har ma sun cafke guda

- Tuni alkali ya maka shi gidan kurkukuku bayan da 'yan sanda suka gurfanar da shi

Kotu to ingiza keyar wani matukin babur mai kafa uku mai suna Ayuba Bashiru zuwa gidan yarin Kirikiri bisa shirya makircin da sacewa tare da yiwa wata ‘yar karamar yarinya mai shekaru 13 fyade.

‘Dan a daidaita-sahu ya tsula tsiya amma ya shiga hannu
‘Dan a daidaita-sahu ya tsula tsiya amma ya shiga hannu

Kotun majistire mai zamanta a Ikeja ta jihar Legas karkashin mai shari’a P. E. Nwaka, ya bayar da umarnin aikewa da fayal din shari’ar zuwa ga ofishin shugaban sashin bayar da shawarwari wajen yanke hukunci (DPP) na jihar domin shawara kan hukuncin da ya dace kafin ranar 16 ga watan Yuli domin cigaba da shari’ar.

Bashiru wanda ya kasance mazaunin gida mai lamba 42 ne a unguwar Owoduni St., Ajegunle a jihar ta Legas, ana tuhumarsa ne da laifin shirya makirci da sacewa tare da fyade.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam

Da farko dai ‘dan sanda mai gabatar da kara sufeto Christopher John ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a makwancinsa tare da taimakon wasu da yanzu haka sun tsere a tsakanin ranar 31 ga watan Mayu zuwa 2 na watan Yuni.

Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin da abokan aikata masha’ar tasa sun kame yarinyar ne yayinda take hanyarta ta zuwa aiken da mahaifiyarta tayi mata.

Kuma sun tsare yarinyar ne har tsawon kwana biyu a gidan nasa, suka kuma tilasta yin lalata da ita ta karfin tsiya.

wannan dai laifi ne da ya saba da sashi na 260 na kundin manyan laifuka na jihar Legas na shekara ta 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng