Wani kwamishina a kudancin Najeriya ya sauka sheka daga PDP zuwa APC
- Wani kwamishinan gwamna Dickson na Jihar Bayelsa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Kazalika, wani tsohon direktan cigaban matasa a gwamnatin Dickson shima ya fice daga PDP ya koma APC tare da magoya bayansa
- APC tayi maraba da sabbin mambobin inda tace za ta fatattaki PDP daga Jihar Bayelsa a shekarar 2020
Rahotanni da muka samu sun ce kwamishinan cigaban matasa, Otobo Ibarakumo ya yi murabus daga mukaminsa a karkashin gwamnatin gwamna Dickson na Jihar Bayelsa.
Ibarakumo tare da dimbin magoya bayansa sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC ne a ranar 20 ga watan Yuni kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA: An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya
Baya ga Ibarakumo da magoya bayansa, Legit.ng ta gano cewa wani tsohon direktan cigaban matasa a gwamnatin gwamna Dickson da ke daga karamar hukumar Nembe shima ya fice daga PDP ya koma APC tare da magoya bayansa.
A wata gagarumin biki da akayi a sakatariyar APC da ke Yenizue-Gene, Yenagoa, shugabanin jam'iyyar da dama ne suka hallara don yin maraba da wadanda suka baro jam'iyyar PDP don shigowa APC.
Cikin wanda suka hallarci taron har da dan majalisar jiha mai wakiltan yankin Brass 1, Isreal Sunny-Goli da kuma abokin takarar tsohon gwamna Timipre Sylva a zaben 2015, Wilberforce Igiri da ciyaman din jam'iyyar APC na jihar, Jonathan Amos da dan kwamitin amintatu, Peres Peretu.
A jawabinsa na maraba da sabbin mambobin, Cif Timipre Sylva wanda ya samu wakilcin Sunny-Goli ya taya su murnar ficewa daga PDP.
Ya kuma ce tabbas APC ne za ta karbe gidan gwamnatin jihar a shekarar 2020 tare da kira ga yan jam'iyyar su hada karfi da karfe don ganin sun kayar da PDP.
Ya ce gwamnatin PDP tana wahal da mutanen jihar ne kawai domin babu wani abin da ta tabuka inda ya ce mutanen jihar na fama da talauci da rashin ababen more rayuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng