Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwa da neman iri ga Goodluck Jonathan (Hotuna)

Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwa da neman iri ga Goodluck Jonathan (Hotuna)

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai ziyara zuwa gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a gidansa dake garin Yenagoa na jihar Bayelsa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A jawabinsa, Atiku ya bayyana bacin ransa da yadda jam’iyyar APC ta gaza cika alkawarin da ta daukar ma yan Najeriya, musamman matsalar rashin aikin yi, tabarbarewar tattalin arziki tare da matsalar tsaro, inji rahoton majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Hankula sun tashi yayin da jama’a suka ci karo da Bom a sakatariyar jam’iyyar PDP

Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwa da neman iri ga Goodluck Jonathan (Hotuna)
Atiku da Jonathan

“Jam’iyyar PDP ce kadai ke da karfin komawa Aso Rock, don kuwa babu wata jam’iyya da ta kaita soyuwa a zukatan yan Najeriya, don kuwa da bad an PDP ba, APC ba ta isa ta dare karagar mulki ba, na san cewa a zamaninmu ba’a taba samun matsalar tsaro haka ba, kuma naira bata taba karyewa ba kamar haka, don haka bana jin dadi.” Inji shi.

Shi kuwa a nasa jawabin, tsoho shugaban Jonathan ya bayyana cewa a yanzu jam’iyyar PDP ya kawar da dukkanin matalolinta, tun lokacin da ta kawar da matsalolin da suka dabaibayeta bayan ta fadi zaben 2015, don haka lokaci yayi da zata sake darewa kujerar shugaban kasa.

Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwa da neman iri ga Goodluck Jonathan (Hotuna)
Atiku da Jonathan

“Na gamsu da maganan Atiku na cewa babu wata jam’iyya da ta kai PDP a yanzu duk da cewa tana adawa ne, mun san abinda ya karya mu a zaben shekarar 2015, don haka ba zamu maimaita kuskurenmu ba a zaben 2019.” Inji shi

Bayan ziyarar da ya kai ga Jonathan, Atiku ya garzaya fadar gwamnatin jihar Bayelsa, inda ya gana da gwamnan jihar, Seriake Dickson, sa’annan ya nemi goyon bayansa akan manufarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwa da neman iri ga Goodluck Jonathan (Hotuna)
Atiku da matar Jonathan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel