An fara: Atiku ya fara rangadin neman goyon baya don tsayawa takara, ya nada sarkin yakin neman zaben sa
Tsohonn mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fara rangadin jihohin Najeriya domin neman goyon bayan masu fada a ji a PDP a kokarin sa na son ganin jam’iyyar ta tsayar das hi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
Atiku ya ziyarci gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a jiya, Talata, inda bayan ganawar su ya yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki da ta bi sahun PDP wajen karbar sakamakon zabe da zuciya daya kamar yadda PDP din tayi a zaben shugaban kasa na 2015.
Tuni Atiku ya nada tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel, a matsayin sarkin yakin neman zaben sa.
A yau, Laraba, Atiku ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, a gidan sa dake jihar sat a haihuwa, Bayelsa.
A yayin ziyarar ta sa, Atiku, ya bayyana Jonathan a matsayin gwarzon siyasa da tarihi ba zai taba mantawa da halin dattako day a nuna na karbar sakamakon zaben 2015 ba tare da kokarin tauye sakamakon ko juya alkaluma ba.
DUBA WANNAN: Katobara: Allah-n da ya yi mana maganin mulkin Abacha, shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo
Da yake mayar da martini, Jonathan ya yabawa Atiku bisa nadin Gbenga Daniel a matsayin sarkin yakin neman zaben sa, tare da bayyana cewar ya nada mutumin day a dace a lokacin day a dace.
A nasa jawabin, Gbenga Daniel, ya jinjinawa Jonathan a matsayin shugaban kasar Najeriya mafi ilimi da kuma gogewa a siyasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng