Zamu iya kare dukkan gyare-gyaren da muka yi a kasafin kudin 2018 - Majalisa ta fadawa Buhari
Majalisar Wakilai ta ce zata iya kare dukkan canje-canjen da su kayi a kasafin kudin shekarar 2018 da shugaba Buhari ya rattaba hannu a kai a yau.
Mai magana da yawur majalisar, Abdulrazak Namdas ne ya fadi hakan bayan shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin na N9.12 tiriliyan.
Shugaba Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda yan majalisar su kayi canje-canje a kasafin kudin, har sun kara saka sabbin ayyuka guda 6,403 a kasafin kudin.
KU KARANTA: An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya
Namdas ya mayar da martani inda ya ce 'yan majalisan suma suna "aikin da aka zabe su suyi ne ".
Ya kuma ba laifin yan majalisar bane tsaikon da ake samu wajen gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin daga watan Janairu zuwa Disamba wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da shugaba Buhari ya koka a kai.
Ya ce shugabanin ma'aikatu da hukumomi da cibiyoyi ne ke da alhakin ganin sun zartas da ayyukan da ke kasafin kudin.
Ya ce majalisar tana godiya ga shugaba Buhari kan yadda ya rattaba hannu kan kasafin kudin sai dai akwai wasu abubuwa da ya ke son jawo kan hankalin mutane kai;
"Fadar shugaban kasa ke shirya kasafin kudi sai dai dokar kasa ta bawa majalisa damar su tattance kasafin kuma suyi canje-cenje inda ya dace, irin wannan canje-canjen ne ya sanya shugaba Buhari kokawa kan kasafin kudin.
"Shugabanin hukumomi da ma'aikatu da cibiyoyi ne suka janyo rashin rattaba hannu kan kasafin kudin domin basu gabatta gaban majalisar don kare kasafin kudaden nasu a kan lokaci ba.
"Ya kuma kare karin N14.5 biliyan da majalisar tayi da cewa kain da su kayi bai kai adadin da majalisar ta ware ba kafin shekarar 2015.
"Game da sabbin ayyukan da muka kara, muna tunatar da shugaban kasa cewa mu wakilan jama'a ne kuma mun lura cewa wasu daga cikin ayyukan da ke cikin kasafin kudin ba za su isa ga talaka ba shiyasa mu kayi wannan karin.
Daga karshe mai magana da yawun majalisar ya ce majalisar na maraba da kasafin kudi na cike gibi da shugaban kasa zai sake turowa kuma tana godiya kan irin fadar shugaban kasar ke aiki tare da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng