Yadda Tauraruwar Ronaldo ke ci gaba da haskawa a Gasar Kofin Duniya

Yadda Tauraruwar Ronaldo ke ci gaba da haskawa a Gasar Kofin Duniya

A ranar yau ta Laraba da hausawa kan ce Tabawa ranar samu, fitaccen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Real Madrid watau Cristiano Ronaldo, ya ci ga da kafa taraihai daban-daban a gasar kwallon kafa ta kofin Duniya da ake fafatawa a Kasar Rasha.

Fitaccen dan wasan ya ci gaba da bakantawa 'yan adawar sa kamar yadda ya saba a koda yaushe samakon zuciyar dagiya da jajircewa wajen neman nasara da yake da ita.

A halin yanzu dai gogaggen dan kwallon kafa ya jefa kwalaye 4 kenan cikin wasannin biyu kacal da ya bugawa kasar sa ta Portugal a gasar kofin duniya na 2018.

Ronaldo shi kadai ya jefa kwallaye uku a koma yayin wasan farko da kasar sa ta kara da kasar Spain da suke gurbi daya mai lambar B inda aka tashi kunnen doki.

Hakazalika Ronaldo ya sake jefa kwalo guda yayin wasan su na yau da kasar Morocco wadda ita ma suke gurbi guda inda wannan kwallo ita kadai ce ta tabbatar da nasarar kasar sa yayin da aka tashi ci daya da nema.

Murnar Ronaldo yayin da ya jefa kwallo a ragar Kasar Morocco a Gasar Kofin Duniya 2018
Murnar Ronaldo yayin da ya jefa kwallo a ragar Kasar Morocco a Gasar Kofin Duniya 2018

Legit.ng ta fahimci cewa, Ronaldo ya kafa tarihi a Duniyar kwallon kafa da ya dara kowane dan kwallo da ya taba taka leda a nahiyyar turai wajen tarawa kasar sa kwalaye, inda kwallon da ya kada a wasan su na yau da kasar Morocco ya kai matakin kwala-kwalai 85.

Kwararrun masan kwallon kafa su na mamakin yadda Ronaldo ke ci gaba da zarra gami da fintikau a harkar tamola a halin yanzu da shekarun sa a duniya sun kai 33 da sabawa sunnar sauran 'yan kwallon da suke shude.

KARANTA KUMA: 'Yan Takara 10 na Kujerar gwamnatin Jihar Nasarawa sun amince da dan Takara daya

Bugu da kari Ronaldo shine dan kwallon kafa a matakin na biyu mafi tarawa kasar sa kwala-kwalai yayin da yake biye da fitaccen dan kwallon kafa na kasar Iran, Ali Daei mai tarin kwala-kwalai 109.

Rahotanni daga kafofin watsa labarai da dama na duniya sun kuma bayyana cewa, ba bu wani kwallon kafa da tauraruwar sa ta kai ta Ronaldo haskawa a halin yanzu da ake ci gaba da fafata gasar kofin Duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng