An tursasa ni sanya Hannu kan Kasafin Kudin 2018 - Buhari

An tursasa ni sanya Hannu kan Kasafin Kudin 2018 - Buhari

Daga karshe an samu Najeriya ta shigar da kasafin kudin 2018 cikin doka yayin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kansa da misalin karfe 12.05 na ranar yau ta Laraba a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya bayyana, shugaban kasar ya rattaba hannu ne ba tare da halarcin shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Wadanda suka halarci wannan fadar shugaban kasar yayin bikin rattaba hannu kan kasafin kudin sun hadar da; Honorabul Mustapher Dawaki, Sanata Ita Enang, Sanata Danjuma Goje, Honarabul Alhassan Ado-Doguwa, Mallam Abba Kyari da kuma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

A yayin rattabu hannu kan kasafin kudin da misalin karfe 12.05 na ranar yau ta Laraba, shugaba Buhari ya bayyana cewa an tursasa aiwatar da hakan ne sakamakon gujewar kawo tsaiko na tattalin arzikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Saraki ya Jagoranci tawagar Majalisar Dattawa zuwa Kasar Rasha

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne sakamakon fushin sauye-sauyen da Majalisar Dokoki ta tarayya ta gudanar a cikin kasafin kudin sabanin wanda ya gabatar a gaban ta.

Cikin fushi shugaba Buhari ya soki majalisar Dokoki ta tarayya na sauye-sauyen cikin kasafin kudin musamman a wasu ma'aikatu muhimmai na kasar da zai bayar da wani tasari na daban ga tattalin arzikin kasar nan.

A yayin haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya jagoranci tawagar wasu 'yan Majalisar zuwa kasar Rasha inda zasu gana da Majalisar kasar domin inganta dankon zumunta da dangartaka tsakanin kasashen biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng