NIS ta gargadi wanda ba 'yan kasa ba su nisanta kansu da zaben Najeriya

NIS ta gargadi wanda ba 'yan kasa ba su nisanta kansu da zaben Najeriya

Hukumar kula da shige da fice na kasa wato 'Nigeria Immigration Service (NIS), tayi gargadi da mutanen da ba yan kasa ba su guji kutsa kai cikin harkokin zaben Najeriya ko kuma jefa kuri'a.

A wata sako da ta fito daga kakakin hukumar NIS, DCI S James, Shugaban NIS na kasa, Muhammed Babandede ya samu wasu rahotanni da suka nuna cewa ana yiwa wasu bakin haure rajistan zabe a Najeriya.

NIS ta gargadi wanda ba 'yan kasa ba su nisanta kansu da zaben Najeriya
NIS ta gargadi wanda ba 'yan kasa ba su nisanta kansu da zaben Najeriya

Bayan kula da shige da fice na mutane da hukumar keyi, aikin ta ya hada da tabbatar da cewa babu wani bako da ya jefa kuri'a a zaben Najeriya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Bayan tura masu sanya idanu a kan zabubuka da hukumar za tayi, za kuma ta fara gangamin wayar da kan mutane saboda a hana wadanda ba yan kasa ba jefa kuri'a a zabukan Najeriya.

Hakan yasa hukumar ta NIS ke hadin gwiwa tare da hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC wajen ganin babu wani wanda ba dan kasa ba da akayi wa rajista cikin sunayen masu zabe na kasa.

Hukumar ta NIS kuma tana kira ga 'yan Najeriya su sanar da hukumar idan suna zargin akwai wani wanda ba dan kasa ba da ke kokarin rajista ko kuma jefa kur'a a zabukan Najeriya a kan lambar wayar kamar haka 07080607900 ko kuma email nis.servicom@nigeriaimmigration.gov.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel