Hayaƙin Janareta ya kar wata Uwa da 'Ya'yan ta 5 a jihar Edo

Hayaƙin Janareta ya kar wata Uwa da 'Ya'yan ta 5 a jihar Edo

Wani Magidanci Tochukwu Okwueze, ya gamu da ibtila'in Duniya yayin da ya rasa iyalan sa baki daya lokaci guda sakamakon shakar hayaƙin Janareta da suka yi a jihar Edo dake Kudancin Najeriya.

Okwueze ya rasa Uwargidan sa da 'ya'yayen su biyar yayin da makwabta suka yi kacibus da gawar su kwankwance cikin gidan su a ranar Talatar da ta gabata.

Wannan lamari dai ya afku ne a Unguwar Akpata dake karamar hukumar Egor ta jihar Edo da a yanzu wannan Magidanci na kwance a gadon Asibiti inda likitoci ke fafutikar ceto rayuwar sa kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, makwabta sun yi kacibus da gawarwakin wannan iyali da safiyar ranar Talatar da gabata yayin da suka balle kyauren gidan su.

Hayaƙin Janareta ya kar wata Uwa da 'Ya'yan ta 5 a jihar Edo
Hayaƙin Janareta ya kar wata Uwa da 'Ya'yan ta 5 a jihar Edo

Bincike ya tabbatar da cewa, hayakin Janareta ne ya rika kurdadowa zuwa makwantar wannan mamata sakamakon rashin wuta da ya sanya suka bar shi a kunne har zuwa wayewar gari.

KARANTA KUMA: Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi

Legit.ng ta fahimci cewa, karar kwana ta sanya ajali bai cimma wannan Magidanci ba yayin da aka garzaya da shi cikin gaggawa zuwa wasni asibitin kudi inda Likitoci ke fafutikar ceton ransa.

Hakazalika kwamishinan 'yan sanda na jihar, Johnson Kokumo, ya tabbatar da afkuwar wannan tsautsayi da mai ban tausayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel