Shugaban CAN ya yi magiya ga Buhari kan hukuncin kisa da Kotu ta yanke ma wasu Kiristoci 5 da suka kashe dan Fulani

Shugaban CAN ya yi magiya ga Buhari kan hukuncin kisa da Kotu ta yanke ma wasu Kiristoci 5 da suka kashe dan Fulani

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya-CAN, Fasto Supo Ayokunle ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya baki kan hukunci kisa da wata Kotu ta yanke ma wasu matasa kiristoci guda biyar, bayan ta kamasu da kashe wani makiyayi a jihar Adamawa.

Mutanen da Kotu ta yanke ma hukunci sun hada da Alex Amos, Alheri Phanuel, Holy Boniface, Jery Gideon, da Jari Sabagi, inda ta tabbatar da cewa sun kashe wani Bafulatani makiyayi mai suna Adamu Buba da yan uwansa uku, wanda suka jefa gawarsa cikin ruwa.

KU KARANTA: Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

https://www.youtube.com/watch?v=FMiXNSPhBlo

Ayo ya bayyana haka ne a ranar Talata, 20 ga watan Yuni a babban birnin tarayya Abuja, inda yace; “Rahotanni sun tabbatar da mai sharia Abdul Azeez Waziri na babbar kotun jihar Adamawa ya yanke hukuncin kisa ga Alex Amos, Alheri Phanuel, Holy Boniface, Jery Gideon, da Jari Sabagi.

“ A cewar Kotun sun kashe wasu makiyaya guda 3 a ranar 1 ga watan Yuni an shekarar 2017, a kauyen Adamun cikin karamar hukumar Demsa, tare da kashe shanu da dama. Duk da cewa bamu goyon irin wannan kisa, amma muna sane da yadda ake kashe Kiristoci a duk fadin kasar nan.

“Musamman a jihar Kaduna, Benuwe, Taraba, Filato, da Enugu, kuma mutanen dake aikata wannan ta’asa Fulani ne makiyaya, amma har yanzu ba’a taba kama sub a, don haka muke mamakin yadda aka yi aka kammala shari’ar mutanen nan cikin kankanin lokaci.” Inji shi.

Daga karshe CAN ta tuna ma Buhari maganan da suka ce shugaban kasar Amurka ya fada masa a yayin ziyarar da ya kai Amurka, cewa ya gargade shi akan ba zasu yarda da yadda ake kashe Kiristoci ba a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng