An gano wani bayahuden Minista da yake yi wa kasar Iran leken asiri

An gano wani bayahuden Minista da yake yi wa kasar Iran leken asiri

- Wani tsohon Ministan Israila na yi wa Iran leken asiri

- An gano A Najeriya suka dauke shi aiki

- An same shi da halayen marasa gaskiya, kuma an kwace lasisin sa

An gano wani bayahuden Minista da yake yi wa kasar Iran leken asiri
An gano wani bayahuden Minista da yake yi wa kasar Iran leken asiri

Kasar Israila, ta Yahudu, ta kama wani tsohon ministanta da laifin leken asiri, da ma taimakawa abokan gaba a lokacin yaki, indaaka gano yana sayar ma da kasar Farisa bayanan sirri na soji da gwamnatin kasarsa, ga kasar Iran.

Gonen Segev, ya fara sayar da bayanan ne bayan da ya taba yin minista a 1990, sannan aka kama shi da laifukan damfara da cuwa-cuwa, laifi da ya kaishi ga zaman kurkuku na shekaru biyar.

Sai dai bayan da ya fito, ya koma Najeriya da zama, inda aka gano ashe bayanan sirri yake sayar wa kasar Iran.

DUBA WANNAN: APC ta hakura ta mika mulki in ta fadi zabe

An dai kama shi a kasar Equatorial Guinea, yana kokarin sayar da wasu bayanan na sirri, kuma tuni aka cacume shi zuwa kasar sa ta haihuwa, domin fuskantar kuliya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng