'Yan sandan Legas sun bankado wata makarkashiyar sace ma'aikaciyar kwastam

'Yan sandan Legas sun bankado wata makarkashiyar sace ma'aikaciyar kwastam

Hukumar Yan sandan Najeriya ta ce jami'an ta da ke aiki da Area D a unguwar mushin sun bankado wata makarkashiyar sace wata mataimakiyar Comptroller na kwastam tare da dan ta da kanin ta a ranar Asabar 16 ga watan Yuni.

Sashin rundunar Yan sandan na gagawa (RRS) na jihar Legas ne suka bayar da wannan sanarwan a ranar Litinin 81 ga watan Yuni ta shafinsu na Twitter @rrslagos767.

Sai dai ba'a bayyana sunan jami'an kwastam din ba a rubutun na Twitter.

'Yan sandan Legas sun bankado wata makarkashiyar sace ma'aikacin kwastam
'Yan sandan Legas sun bankado wata makarkashiyar sace ma'aikacin kwastam

KU KARANTA: Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

A cewarsa yan sandan, wanda ake tuhuma da laifin satar mutanen sun hadu ne da kanin jami'an kwastam din, Yisa Theophilus, inda su kace za su sayar masa da fili.

Wanda ake zargi da yunkurin satar mutanen wani matashi ne mai suna Yomi Odudare wanda ya yi kaurin suna wajen aikata laifuka a Legas din.

Bayan anyi ram dashi, Mr Odudare ya amsa cewa ya hada baki da wani tsohon direban mataimakiyar Comptroller din na kwastam mai suna Olugbenga Kehinde Ojo wajen sace jami'an kwastam din.

A yayin da suka bayar da bayanin yadda suka kama mai garkuwa da mutanen, Yan sandan karkashin umurnin Kwamishinan Yan sanda Imohimi Edgal sun amsa sunyi dabara inda suka amsa wayar Mr Theophilus.

Daga bisani Yan sandan suka bi Mr Theophilus wurin da mai kiran wayar ya ce su hadu kuma anan ne aka damke shi kuma bayan bincike aka gano dama can mai laifi ne.

Wanda ake tuhumar ya amsa cewa dama tun farko niyyarsa shine ya sace kanin jami'an kwastam din don itama daga baya su sace ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel