Kotu ta bayar umarnin daure wani dan kasuwa da ya saci akuya

Kotu ta bayar umarnin daure wani dan kasuwa da ya saci akuya

Alkalin kotun Doma da ke Gombe ya bayar da umurnin a tsare wani dan kasuwa mai shekaru 20 a gidan yari saboda satar akuya.

Wanda ake tuhuma mai suna Abubakar Adamu da ke zaune a London quarters ya saci akuya mai launin ruwan kasa wanda kudinta ya kai N15,000 mallakar Umar Abubakar da ke zaune a Kasuwar Mata quarters duk dai a Gombe.

Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

Dan sandan mai shigar da kara, Saja Mohammed Aliyu ya ce abin ya faru ne a ranar 17 ga watan Yuni.

Kotu ta bayar umarnin daure wani dan kasuwa da ya saci akuya
Kotu ta bayar umarnin daure wani dan kasuwa da ya saci akuya

Ya cigaba da cewa wanda ake tuhumar ya sace akuyar kuma ya yanka, sannan ya tafi da ita zuwa kasuwar mata inda ya siyar wa mahauta.

Mahautan sun tsargu saboda yadda suka lura Mr Adamu yana kokarin sayar da akuyar a farashi mai rahusa, hakan yasa su kayi tunanin akwai magana a kasa.

Alkalin kotun, Aminu Haruna, ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni amma ya bayar da umurnin a bawa wanda ake zargin masauki a gidan yari.

A wata labarin, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tura wakilansa zuwa Jihar Bauchi don yin ta'aziyya ga iyalan wanda iftila'in gobara da iska mai karfi ta yiwa barna.

Iskar mai karfi ta rushe gidaje da dama tare da sanadiyyar rasuwar mutane takwas.

Gobara kuma ta afku a kasuwar garin Azare inda ta lalata shaguna da dama a kasuwar.

Shugaban hukumar bayar da agajin gagawa na kasa NEMA, Alhaji Mustapha Maihaja yana cikin tawagar da za su kai ziyarar Bauchi karkashin jagorancin Ministan Ilimi Adamu Adamu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: