Tashin hankali: Mutuwar wata babbar likita ta saka wani likita da wasu Nurse biyu yanke jiki su fadi kasa sumammu

Tashin hankali: Mutuwar wata babbar likita ta saka wani likita da wasu Nurse biyu yanke jiki su fadi kasa sumammu

An samu rudani da dimuwa a sabitin kwarraru na jihar Kogi dake garin Lokoja yayin da wani likita da wasu Nurse biyu suka yanke jiki suka fadi sumammu bayan samun labarin mutuwar wata babbar likita, Chukwudibe Rosemary, dake shugabantar sashen kula da kananan cututtuka a asibitin.

Rosemary ta mutu ne ranar 18 ga watan Yuni bayan duk kokarin abokan aikin ta na ceto ran ta daga ciwon bugun zuciya ya ci tura.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewar bayan mutuwar Rosemary ne, sai wani likta a asibitin, Dakta idris Nuhu, tare da wasu Nurse uku suka yanke jiki suka fadi a sume lokaci guda.

Tashin hankali: Mutuwar wata babbar likita ta saka wani likita da wasu Nurse biyu yanke jiki su fadi kasa sumammu
Tashin hankali: Mutuwar wata babbar likita ta saka wani likita da wasu Nurse biyu yanke jiki su fadi kasa sumammu

Wani rahoto da kungiyar likitoci a jihar ta fitar ta bakin sakataren kungiyar, Dakta Moses Adaudi, ya bayyana cewar, yanzu haka an kwantar da ma’aikatan a asibitin domin basu kulawa ta musamman tare da Karin bayanin cewar, likitan ya suma ne saboda girgiza shi da mutuwar likitar tayi.

DUBA WANNAN: Abinda kasar Amurka ta fada a kan harin da Boko Haram ta kai Damboa daren Asabar

Dakta Adaudi ya kara da cewa likita Rosemary ne ta mutu ne saboda rashin sashen bayar da agajin gaggawa na musamman a asibitin tare da bayyana cewar suman da Nurse din suka yi ba zai rasa nasaba da aiki day a yi masu yawa ba.

Wasu ma’aikatan asibitin sun bayyana cewar Rosemary ta mutu ne saboda ba a biya ta albashin watan Maris ba har yanzu, kuma da kudin take amfani domin sayen magungunan da take amfani da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel