Hotuna: Tinubu ya hadu da Atiku a filin jirgin sama na Akure
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya tafi Akure, babban birnin jihar Ondo domin jagorantar gangamin kujerar gwamnan PDP a jihar dake makwabtaka wato jihar Ekiti.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu babban jigon jam’iyyar APC, mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu maso yamma, Cif Pius Akinyelure; da Gamna Rotimi Akeredolu sun kasance a filin jirgin saman Akure, suma suna shirin tafiya Ekiti domin gangamin neman zaben Kayode Fayemi.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa lokacin da suka ji labarin isowar Atiku, sai suka yanke shawarar tsayawa domin su bashi tarba na musamman.
Tsohon gwamna Gbenga Daniel, wanda a yanzu shine daraktan yakin neman zaben Atiku sai ya gabatar da mutanen biyu cikin ba’a.
KU KARANTA KUMA: Gobara ya tashi a kasuwar Bauchi inda shaguna 500 suka kone kurmus
Haduwar ta su ya kasance cikin karamci sannan sunyi raha duk da cewar kwanakin baya Atiku ya sauya sheka daga APC zuwa PDP sannan kuma yana yawan sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke mulki karkashin lemar APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng