Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a titin Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar

Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a titin Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar

Hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC reshen Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar mutane 11 a wani mummunan hatsarin mota daya faru a ranar Lahadi.

Kwamandan hukumar, Godwin Ngueku, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai (NAN) cewa wata mota kirar Peugeot dauke da fasinjoji tayi karo da wata tipa a babban titin Katsina - Jamhuriyar Nijar.

Ya ce: "Hatsarin ya faru ne misalin karfe 8 na dare a titin Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar. Dukkan mutanen da ke cikin motar sun mutu nan take.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

"An tafi da gawawakin su zuwa babban asibitin Katsina misalin karfe 9 na daren Lahadi kuma iyalansu suna ta zuwa suna daukan gawawakin domin a birne su."

Anyi wata mummunar hatsarin mota a Jihar Katsina
Anyi wata mummunar hatsarin mota a Jihar Katsina

Ngueku ya yi kira ga iyaye su gargadi yaransu a kan tukin ganganci da kuma shaye-shayen ababen maye yayin da za suyi tuki.

A wata rahoton kuma, mutane 10 ne suka mutu sakamakon bullowar cutar amai da gudawa a garin Bida dake Jihar Neja.

Sakataren karamar hukumar Bida, Suleiman Sheshi ya ce a kalla mutane 60 ne aka tabbatar suna dauke da cutar a asibitin Umaru Sanda da ke Bida.

Ya kuma ce akwai wasu marasa lafiyan da ke jinya a wasu asibitocin.

Sheshi ya kuma koka kan yadda likita guda daya ne kadai ke aiki lokacin da ya ziyarci babban asibitin na Bida, ya kuma lura cewa babu isasun kayayakin aiki a asbitin.

Sakataren ya yi kira da gwamnatin jihar ta kai musu dauki domin karamar hukumar ba za ta iya sauke wannan nauyin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: