Gobara ya tashi a kasuwar Bauchi inda shaguna 500 suka kone kurmus
Gobara ya tashi a babban kasuwar garin Azare, karamar hukumar Katagum dake jihar Bauchi, inda dukiyoyi na miliyoyin naira suka halaka.
An rahoto cewa gobaran ya fara ci ne daga misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi, 17 ga watan Yuni har zuwa safiyar ranar Litinin 18 ga watan Yuni.
Akalla sama da shaguna 500 ne suka kone kurmus a ibtila’in da ya afkawa kasuwar.
Mummunan al’amarin na zuwa ne kwana daya bayan guguwar iskar ruwa ya lalata gidaje da sauran kadarorin mutane a ranar Asabar, 16 ga watan Yuni.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa
Mutane da dama sun halaka a guguwar iskar ruwan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng