Magoya bayan Saraki sun yiwa Buhari da IGP ruwan Alkunut (hotuna)
Kamar yadda kuka sani ana cigaba da takun saka tsakanin sufeto janar na yan sanda da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki.
Hakan ya samo asali ne sakamakon zargin Saraki da ake yi bayan yan fashin Offa da aka kama sunce shine ke daukar nauyin su.
Har mun ji cewa Shugaban hukumar yan sanda Ibrahim Idris yayi tattaki har fadar shugaban kasa domin neman yardarm shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen gudanar da bincike akan Saraki.
Mun ji cewa Buhari ya lamunce masa inda yace babu wanda yafi karfin doka.
Sakamakon haka ne magoya bayan Saraki a jihar Kwara suka yi ruwan Alkunut akan shugaban kasar da Sufeto janar na yan sandan.
Shafin Rariya ta wallafa hotunan mutanen rike da littafi mai tsarki yayinda suka gudanar da Alqunut din.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari a jihar Kano
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng