Dakarun Soji sun samu gagarumar nasara a wasu karanbatta da suka sha da yan bindiga a Benuwe

Dakarun Soji sun samu gagarumar nasara a wasu karanbatta da suka sha da yan bindiga a Benuwe

Dakarun rundunar Sojin kasa ta samu gagarumar nasara a wasu karanbatta da ta sha tsakaninta da wasu gungun yan bindiga daban daban a jihar Benuwe, inda aka yi dauki ba dadi, aka kai gwauro aka kai mari, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kaakakin rundunar Sojin, Birgediya Texas Chukwu ne ye sanar da haka, inda yace Sojoji sun yi kicibus da yan bindiga a ranar 14 ga watan Yuni a kauyen Kwatan Gemu, suka kashe wasu daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka tsira da harbin bindiga a jikkunansu, suka jefar da baburansu guda hudu.

KU KARANTA: Wani matashi ya sake kashe kansa a masallacin Makkah

Dakarun Soji sun samu gagarumar nasara a wasu karanbatta da suka sha da yan bindiga a Benuwe
Yan bindiga a Benuwe

Hakazalika a wani hari makamancin wannan da Sojoji suka kai ma yan bindigar jihar Benuwe, Sojojin sun samu nasarar damke yan bindiga guda hudu, tare da kwato bindigu guda bakwai, alburusai, wayoyi biyu da wasu muhimman takardu.

Kaakaki Texas ya cigaba da bayyana yadda Sojoji suka ragargaji wasu gungun yan bindiga a dajin Kawuri na jihar Benuwe, inda suka tarar da bindiga kirar AK 47 da alburusanta, sai dai yace bincike ya nuna cewa wasu mazauna kauyen Suraja, Abiso Ali da Samaila ne ke da mallakin makaman.

Dakarun Soji sun samu gagarumar nasara a wasu karanbatta da suka sha da yan bindiga a Benuwe
Makamai

Daga karshe Birgediya Texas yayi kira ga jama’a da su dinga lura da masu shiga kauyukansu don kai ma jami’an tsaro bayanai game da duk wani da basu gane take takensa ba/

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel