Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kada ya sake tsayawa takara a 2019

Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kada ya sake tsayawa takara a 2019

Kamar yadda muka sani dai tuni shugaba Buhari ya bayyana ra'ayin sa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan da za'a gudanar a shekarar 2019 mai zuwa a kwanan baya a yayin da yake yiwa 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar sa ta APC bayani.

Shi dai shugaban kasar ya ayyana cewa yana so ne ya sake tsayawa takara domin a cewar sa, ayyukan alherin da ya dauko yi a kasar bai kammala su ba sannan kuma yana so ya kara shimfida wasu sabbin ayyukan kuma.

Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kada ya sake tsayawa takara a 2019
Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kada ya sake tsayawa takara a 2019

KU KARANTA: Sabon harin bam ya kashe mutane 31 a Borno

To sai dai kamar a dukkan sauran lamuran kasar musamman ma na siyasa, kudurin na sa ya gamu da yabo da kuma fallasa daga bangarorin da ke goyon bayan sa da kuma adawa da shi akan hakan.

Wannan ne ma ya sanya wasu daga cikin dattawan kasar fitowa domin bayyana ra'ayoyin su game da hakan.

Legit.ng kamar kullum ta tattaro mana wasu daga cikin dattijan na Najeriya da suka nuna matukar adawar su ga kudurin na shugaba Buhari na tazarce, kuma gasu kamar haka:

1. Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo

2. Shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa Alhaji Tanko Yakasai

3. Tsohon ministan lafiya Farfesa A. B. C Nwosu

4. Tsohon gwamnan jihar Anambara Cif Chukwuemeka Ezeife

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng