Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda a kan cin hancin N50, duba hotuna

Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda a kan cin hancin N50, duba hotuna

Wani dan sandan Najeriya mai suna Kehinde Agbede ya shiga shafukan sada zumunta bayan an dauki wasu hotunan shi yana kokawa da wata mai goyo bayan ya sharara mata mari har saida sawun yatsan sa suka fito a fuskar ta.

Kamar yadda wani ma’abocin amfani da dandalin sada zumunta na tuwita, @bolaNlee_c, da ya yada hotunan, y ace lamarin ya faru ne a Mokola dake Ibadan a jihar Oyo. Ya bayyana cewar, dan sandan ya fusata ne saboda matar ta fada masa cewar ya kula lada ya haddasa hatsari a kan titi saboda karbar cin hancin N50.

Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda a kan cin hancin N50, duba hotuna
Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda

Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda a kan cin hancin N50, duba hotuna
Motar su dan sanda Kehinde

Wata matar aure mai goyo ta sha marin wani gardin dan sanda a kan cin hancin N50, duba hotuna
Fuskar matar aure mai goyo da ta sha marin wani gardin dan sanda

Ba a bayyana sunan matar ba ko kuma abinda ya biyo baya ba bayan marin da matar ta sha. Kazalika ba a bayyana ko labarin afkuwar hakan ta kai ga hukumar ‘yan sanda ba.

DUBA WANNAN: Duba hotonabubuwan tarihi da ban mamaki da aka samu cikin tumbin wata Akuya

@bolaNlee_c ya ce dan sanda Kehinde na aiki ne a sashen yaki da dakile fashi da makami na hukumar 'yan sanda (SARS). Jama'ar Najeriya na yin kira a kafafen sada zumunta da soke sashen saboda rahotannin cin mutuncin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng