Mutane 2 sun jikkata yayin da 'yan Baranda suka gwabza a Birnin Dutse

Mutane 2 sun jikkata yayin da 'yan Baranda suka gwabza a Birnin Dutse

Kamar yadda hukumar 'yan sanda ta jihar Jigawa ta bayyana, a halin yanzu akwai mutane biyu dake kwance a gadon asibiti domin kulawa da lafiyar su sakamakon wata arangama da ta afku tsakanin yan baranda a karamar hukumar Dutse ta jihar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Mista Abdu Jinjiri ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban Birnin jihar na Dutse.

Jinjiri ya bayyana cewa, an kwantar da wannan mutane biyu ne a asibiti sakamakon munanan raunuka da suka samu a sanadiyar afkuwar wannan arangama a ranar Juma'ar da ta gabata tsakanin 'yan baranda a kauyen Limawa dake garin Dutse.

Mutane 2 sun jikkata yayin da 'yan Baranda suka gwabza a Birnin Dutse
Mutane 2 sun jikkata yayin da 'yan Baranda suka gwabza a Birnin Dutse

Legit.ng ta fahimci cewa, anyi amfani da makami na wukake wajen sare-sare yayin afkuwar wannan hargitsi mai munin gaske.

KARANTA KUMA: Lauyan Evans, Ogungbeje, ya janye daga shari'a

Kakakin 'yan sandan da ya gaza bayar da dalilin afkuwar wannan hargitsi ya bayyana cewa, hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren.

Ya kara da cewa, an garzaya da wannan mutane biyu babban asibitin Rasheed Shekoni dake garin Dutse inda suke samun kyakkyawar kulawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng